ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto Abdulmajid Taboot yana fadar haka a jiya litinin 24 ga watan Augusta, ya kuma kara da cewa za’a gudanar da zaben raba gardaman ne a ranar 2 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Shugaban kasar ya kara da cewa manufar rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar ita ce, gudanar da sauye-sauyen na asasi a cikin kundin tsarin mulkin kasar wadanda suka hada da, hana tsoffin abokan tsohon shugaban kasar dawowa kan madafun iko, fayyace ayyukan shugaban kasa, da majalisar dokoki da kuma tabbatar da ‘yencin ma’aikatar sharia daga gwamnatin kasar.
342/